Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Abdollahian ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Candith Mashego-Dlamini, mataimakiyar ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu a birnin Tehran a ranar jiya Lahadi.
Jami'iar ta Afirka ta kudu tana iso Tehran tare da wata babbar tawagar kasarta domin tattauna batun taron kwamitin hadin gwiwa na siyasa tsakanin Iran da Afirka ta kudu wanda za a gudanar nan gaba.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce gwamnatin Iran na da mahanga ta musamman dangane da kasar Afirka ta Kudu, inda ya kara da cewa, babu wani shamaki a tsakanin kasashen biyu ta fsuakr dangantakar da ke tsakanin
Amir-Abdollahian ya bayyana dangantakar haɗin gwiwarsu da Afirka ta kudu a matsayin mai tarihi, inda ya ce kasashen biyu na jin dadin yadda wannan alaka take tsawon shekaru da kuma ci gaban da take samu a dukkanin bangarori.
Ya kara da cewa taron hadin gwiwar wanda za a gudanar a birnin Pretoria na da matukar muhimmanci a gare su
A nata bangaren Candith Mashego-Dlamini, mataimakiyra ministan harkokin wajen kasar Afirka ta kudu ta bayyana fatan cewa taron kwamitin shawarwarin siyasa na hadin gwiwa zai gudanar da tattaunawa "mai kyau da inganci" game da batutuwa daban-daban da kuma fitar da sabuwar "taswirar dangantakar kasashen biyu."
Iran da Afirka ta kudu dai suna kyakkyawar alaka a tasakaninsu a dukaknin bangarori na siyasa, harkokin tattalin arziki, cinikayya da kuma musayar ilimin kimiyya da fasaha.
342/